Skip to main content

Shin Akwai Kaman Ceceniya Ko Banbanci Tsakanin Jihadin Shehu Dan Fodio dana Boko Haram?

Originally written by Mubarak Bala for Naij.com on the 7th of May 2017. 


A lokuta da dama, a kowacce al'umma, akan sami masu ikirarin kawo chanji, ko na siyasa, ko na addini, ko al'ada, ko na tattalin arziki. Haka abin yake a addinin Islama, wanda hadisai suke nuni da cewa annabi yace an umarce shi da ya yaqi mutane har sai sun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.

Ya zamo al'ada a musulunce, idan an sami al'umma da bata bi addinin ba, da ayi mata aike na wa'azantarwa, zuwa ga bin abin bautar musulmi, idan al’ummar taqi, akwai zabi, ko ta miqa wuya ta zauna karkashin daular Islama, ta biya harajin jizya, wai shi haraji na dhimmi, ko kuwa a far mata da jihadi, kamar yadda ya faru a garuruwa irinsu Khaybar da Hunaynu, a zamanin da.

Shekaru dari biyu da suka wuce, (1804) a yammacin Sudan, an sami malami da ya kamanta hakan, da sunan jihadi na jaddada addini bayan yayi zargin cewa dagutanci ya shigo ya surka imanin mutane, inda ya tara almajirai mabiya, ya basu tuta, suka bi gari-gari suna kafa daular khalifanci, kamar yadda musulunci ya tanada.

Zuwan turawa a 1903, ya tumbuke wannan daula, ya ture tsarin da suke kai, na zub da jni, cin ghanima, bautar da jama’u, da al’adu, masu bin wasu addinai, ya kawo sabon tsari na ‘yanci ga kowa, musulmi, kirista, maras addini, da ma masu bautar gumaka, a matsayin cewa suna matsayi daya, karkashin Sarautar turawan Ingila. Su wadannan mujahidai, Fulani, aka kore su suka yi gabas da sunan Hijira, zuwa cikin Sudan, kusa da kogin Nilu, wato river Nile a turance.

Sai dai hakan ya bar baya da qura, inda a lokuta da dama, irin masu wannan fahimta ta asalin yadda addininsu ya ce su rayu, ya sa sukan tashi da sunan jihadi, domin dawo da irin wancan tsari na zub da jini, bautarwa, da shugabanci irin yadda musulman farko suka yi shi, mai kyawunsa, da mai muninsa. An sami wani a Kano, a shekarun 1980s, wai shi Muhammadu Marwa, wanda aka yi wa laqabi da maitasine, wanda shima hakan yaso yayi, amma tsarin mulkin zamani ya fi qarfinsa, domin bayyi dabara ta yaqi da kayan zamani ba, sai ya dauki kwari da baka, da takobi, masu bindiga kuwa suka ga bayansa da almajiransa.


A kwanakin nan kuma, sai ga mayaka da suke kiran kansu masu wa'azi, sun taso da niyyar kawar da wannan tsari da suke gani a cewa ba dai-dai yake ba, su a tunaninsu, sai anyi yadda addini yake tun farko, anyi mubayi'a ga Kalifa, ba wai a zabi gwamna ko shugaban kasa ba. Sun zub da jini sosai, sun bautar da jama'a a matsayin kamammun yaqi, sun kuma saci dukiya da sunan ghanima halas, kamar yadda addininsu ya tanadar, sun kuma yi mubayi'a ga irin wannan tsari na zalunci wanda ke kasashen larabawa, wato ISIS, da AlQaida da Taliban, sun kuma barranta da duk wani tsari da yace musulmi da wanda ba musulmi ba, duk daya suke.

Wannan shine irin abun da ya kawo cece-kuce, tsakanin al'ummar musulmi ta Arewacin Najeria, cewa, shin addinin nasu zasu bi da gaske, su bi masu kisan zalunci? Ko kuwa, sabon (tsarin dagutu) na dimokuradiyya zasu bi? Ga dukkan alamu dai, akwai sauran rina a kaba, domin sojojin da mayaqan da masu jihadi ke amfani dasu, su na nan miliyoyinsu, suna zaga al'umma, iyayensu sun watsar dasu, gwamnatoci sun yi biris da ilmin su da rayuwarsu, suna nan basu komai sai jiran abinci, ta kowacce hanya; sune dai Almajirai na Arewar Najeriya.

Comments

  1. I was suggested this web site by my cousin. I'm not sure whether this post is written by him as no one else know such detailed about my difficulty. You are wonderful! Thanks! gmail login

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

Northern Nigerian Muslims and Global Jihadism

Originally written by someone brave, who due to security reasons prefer to remain anonymous.
On Monday the 22nd of May 2017, Salman Ramadan Abedi, a 22-year-old Briton of Libyan ancestry, detonated an improvised explosive device as concertgoers were leaving an indoor arena in Hunts Bank, Manchester, England. Twenty-three people, including Abedi, were killed and approximately 120 were injured. If you are in Nigeria, especially northern part of the country, you may have witnessed several attacks like this in the last years. Although they have subsided in recent times, every now and then one terror attack or another is reported in Northeastern Nigeria. Once again, open condemnations from muslims and non-Muslims have followed the Manchester suicide bombing. Once again, embarrassed muslims (and liberal non-muslims) have come out to show how terrorism has no place in Islam. However, many people disagree and some are polite (or fearful) about this disagreement, including powerful leaders. 
P…

A Chat With THIS IS AFRICA MAGAZINE

Islam is sacrosanct in Northern Nigeria. Suffice to say that denouncing the religion can come with dire consequences. It’s just not something you do. Last year, a young man named Mubarak Bala from Kano bravely did just that. He announced he was an atheist and humanist, and rejected Islam. This came with serious consequences, including alienation from family and friends, physical assaults and death threats. It’s been over a year since this happened and TIA wanted to speak to Mubarak to hear what he had to say and to see how he was doing.


TIA: Please tell us a bit about yourself and your background.


Mubarak Bala: I’m a chemical engineer. I was born in Kano State, northern Nigeria in the mid 80s. I attended the Saudi funded Islamic Foundation Aliyu Bin Abi Talib primary school. I was trained in the Wahhabi Islamic thought, with a jihad ideology. I later attended an all-Muslim private science secondary school, Hassan I. Gwarzo, in Kano State, where Islamic (Qur’anic) study is given a very …

The Almajiri System

Originally posted on: Affairs of Our Nation Saturday September 1st, 2012.

‘Isn’t there present among you, a single good Man!?’No society or nation would prosper, when the so-called elite, do not think for the less endowed majority. Society term all above the age of forty as wise, but I see no wisdom in my society, none in my nation. For how could there be, in a society that condones a system that rots the lives of its children, a staggering 10 million of them (Fed. Min. of Education, 2011 estimate), currently, not to talk of those that grew out of it, and babies yet admitted. Regrettably, apparently everyone had turned a blind eye.

When did a sophisticated system, well intentioned, divert so dismally? I say this is not Islam, because if it were, it would have been practiced in Mecca, Medina, Tehran, Basra, Cairo, Damascus, Dubai, Jakarta or Islamabad. This practice is unique only to black Africa, West Africa to be precise, and where it grinds most; Northern Nigeria, with an estimated po…